Matatar Mai ta Dangote da ke Najeriya, wadda ke da ƙarfin tace gangar mai 650,000 a kowace rana, ta bayyana cewa tana da isasshen man jirgin sama da za ta iya fitarwa zuwa kasuwannin duniya baki ɗaya, in ji Babban Daraktan kamfanin, David Bird.

Bird ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin da yake magana a taron S&P Global Energy Middle East Petroleum and Gas Conference da aka gudanar a birnin London.

Ya ce ƙarancin bukatar mai a nahiyar Afirka idan aka kwatanta da sauran yankuna na duniya ya sa matatar ke samun rarar man da za ta iya fitarwa zuwa ƙasashen waje.

Ya kuma ce man jirgin sama na daga cikin nau’o’in mai da suka fi fuskantar tasiri daga rikicin Iran da kuma rufe Mashigar Hormuz a baya-bayan nan.

Bird ya bayyana cewa matatar na aiki a cikakken ƙarfin da aka tsara mata a halin yanzu, tare da shirin ƙara faɗaɗa ayyukanta a nan gaba.

Ya ce ana shirin wani sabon mataki na faɗaɗa ƙarfin tace mai da ya kira “ruthless replication”, wanda zai ƙara yawan tacewa zuwa ganga 700,000 a kowace rana nan da shekarar 2028.

A cewarsa, an riga an sayo muhimman kayan aikin da ke ɗaukar lokaci mai tsawo kafin isowa, kuma ana ci gaba da shirye-shiryen bayar da kwangilolin gine-gine.

Bird ya kuma ce idan aka ƙara wata matatar a yankin Gabashin Afirka a nan gaba, kamfanin na iya kaiwa ga tace gangar mai har miliyan 2.1 a kowace rana, abin da zai ƙara ƙarfafa matsayinsa a kasuwar duniya.

A ƙarshe, ya ce Najeriya ta sauya daga fuskantar ƙarancin mai zuwa cikakken wadatar mai tun bayan fara aiki da Matatar Dangote.