Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ɗage sauraron shari’ar da Nafiu Bala Gombe ya shigar kan shugabancin jam’iyyar ADC ƙarƙashin Sanata David Mark zuwa ranar 8 ga Yunin da muke ciki .


Kamfanin Dillancin Labarai na kasa (NAN) ya ruwaito cewa Mai Shari’a Peter Lifu ne ya ɗage shari’ar bayan lauyan Gombe, Robert Emukpoeruo (SAN), ya nemi ƙarin lokaci saboda rashin halartar lauyoyin wasu ɓangarorin da ke neman a haɗa su cikin shari’ar.


Yayin zaman kotun, lauyan ADC, Shaibu Aruwa (SAN), ya tunatar da kotun cewa tsohon mai sauraron ƙarar, Mai Shari’a Emeka Nwite, ya riga ya yi la’akari da waɗannan ɓangarorin a zaman da ya gabata.


Ya roƙi kotun ta ba su damar bayyana dalilin da ya sa suke son shiga cikin shari’ar domin tabbatar da adalci ga kowa.

Sai dai lauyan mai ƙarar ya bayyana cewa Kotun Ƙoli ta umarci a gaggauta sauraron shari’ar, don haka ya nemi a ba dukkan ɓangarorin damar kammala shigar da takardunsu kafin a ci gaba da sauraron ƙarar.