Sama da mutum dubu Goma sha uku 13 masu fama da cutar amosanin jini ne ke amfana da kulawa da magani kyauta a karkashin cibiyar Abba Care Sickle Cell Diseases Centre a Jihar Kano.


Shugabar Hukumar Taimakon Lafiya ta Jihar Kano, Dr. Rahila Mukhtar, ce ta bayyana hakan yayin wani gangamin tattaki da aka gudanar a ranar Asabar, a matsayin wani bangare na bikin ranar wayar da kan al'umma kan cutar amosanin jini.


Dr. Rahila ta ce an yi amfani da wannan rana ne wajen jan hankalin jama'a da su kara kaimi wajen ba masu fama da cutar kulawa da goyon baya. Ta kuma yabawa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa irin gudunmawar da yake bayarwa wajen inganta lafiyar masu fama da cutar, musamman ta hanyar samar da cibiyar Abba Care Sickle Cell Diseases Centre.


Wakilinmu Adamu Abdullahi ya rawaito cewa Dr. Rahila ta kara da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da sanya sama da mutum dubu 13 masu fama da cutar amosanin jini cikin shirin Abba Care, inda ake ba su kulawa da magani kyauta.


Ta ce baya ga hakan, akwai kuma shirin Basic Health Care Provision Fund (BHCPF), wanda haɗin gwiwa ne tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatin Jihar Kano, wanda shi ma ke ba masu fama da cutar amosanin jini kulawa da magani kyauta.


Bikin ranar wayar da kan al'umma kan cutar amosanin jini na bana ya samu hadin gwiwar Sickle Cell Foundation Nigeria da kuma ƙungiyoyin da ke kula da masu fama da cutar a matakin duniya.