Gwamnatin Jihar Bauchi ta ba da umarnin rufe Masallacin Ibadurrahman da ke unguwar Shingen Abba a cikin garin Bauchi, sakamakon rikicin da ya daɗe yana ci gaba tsakanin limamin masallacin da kwamitin gudanarwarsa.
An ɗauki matakin ne domin dakile yiwuwar ɓarkewar rikici da ka iya haddasa asarar rayuka da dukiyoyi a tsakanin al’ummar yankin.
Kwamishinan Hisba na Hukumar Shari’ar Musulunci ta Jihar Bauchi, Barrista Aminu Balarabe Isah, ya bayyana wa manema labarai cewa gwamnatin jihar ta ɗauki matakin ne bisa umarnin kotu da kuma la’akari da yanayin rikicin da ya shafe kusan shekaru uku yana gudana.
Ya ce an yi ƙoƙarin sasanta ɓangarorin tun daga shekarar 2023 lokacin da aka gabatar da batun gaban Hukumar Shari’ar Musulunci, amma duk ƙoƙarin sulhu da shimfiɗa hanyoyin zaman lafiya bai kai ga samun mafita mai ɗorewa ba.
A cewarsa, har ma an taɓa dakatar da limamin masallacin na wani lokaci domin rage zafin rikicin, amma bayan dawo da shi bakin aikinsa, matsalar ta sake ɓarkewa.
Barrista Aminu ya jaddada cewa gwamnati ba za ta lamunci duk wani yanayi da zai iya jefa rayukan jama’a cikin haɗari ba.
“Doka ta bai wa kowa damar gudanar da addininsa cikin ’yanci, amma idan hakan zai haifar da rashin zaman lafiya ko barazana ga rayuka da dukiyoyi, gwamnati za ta ɗauki matakin da ya dace domin kare al’umma,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa rufe masallacin mataki ne na wucin gadi har sai an samu mafita ga rikicin da ke tsakanin ɓangarorin biyu.
Haka kuma, ya yi kira ga mazauna yankin da su bi umarnin hukumomi tare da kauce wa duk wani abu da zai iya tayar da tarzoma, yana mai gargadin cewa duk wanda ya karya umarnin rufe masallacin zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.