Hukumar Kula da Lafiya ta Matakin Farko ta Jihar Kano (KSPHCMB) tare da Shugabannin Kananan Hukumomi 44 na jihar sun amince da wani daftarin tsarin aiki mai matakai shida da nufin ƙarfafa ayyukan kiwon lafiya a matakin farko da inganta gaskiya da riƙon amana, da kuma kyautata shugabanci a fannin lafiya a faɗin Jihar Kano.
Wannann na cikin wata Sanarwa da Mai magana da yawun hukumar ta Jihar Kano Sa'adatu Sulaiman ta rabawa manema Labarai.
An cimma waɗannan matsaya ne a yayin taron rabin shekara da aka gudanar na tsawon kwanaki biyu da aka gudanar a Jihar kaduna
Taron ya mayar da hankali kan ne nazari da tantance ayyuka da gwamnatin da masu ruwa da tsaki ke yi a bangaren lafiya, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa domin samar da sakamako mai kyau.
Babban Daraktan ma'aikatar lafiya a matakin farko KSPHCMB, Farfesa Salisu Ahmad Ibrahim, ya jaddada muhimmancin ci gaba da haɗin gwiwa tsakanin Hukumar da Kananan Hukumomi.
Haka kuma, Babban Sakataren Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano, Pharmacist Aminu Bashir, ya yi kira da a ƙara himma wajen tsare-tsare, riƙon amana da kuma aiwatar da shirye-shiryen lafiya yadda ya kamata.
Hon. Aminu Sa'ad Aminu, Dan majalisar mai wakiltar mazabar Ungoggo kuma Shugaban Kwamitin yada labarai na Majalisar dokokin Jihar Kano, ya sake tabbatar da aniyar Majalisar na tallawa manufofi da shirye - shiryen da za su karfafa aiyukan kiwon Lafiya a matakin farko a Jihar Kano