Wakiliya ta musamman ta Majalisar Ɗinkin Duniya kan ’Yancin Addini ko Imani, Nazila Ghanea, ta bayyana cewa rashin hukunta masu aikata laifuka da kuma raunin aiwatar da doka na daga cikin abubuwan da ke ƙara haddasa zarge-zargen tsanantawa da ma kisan kare-dangi a Najeriya.

Ghanea ta bayyana hakan ne bayan wata ziyarar bincike ta tsawon makonni biyu da ta kai Najeriya domin tantance halin da ake ciki dangane da ’yancin addini da zaman tare tsakanin al’ummomi.

Ta ce yawaitar hare-haren ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da kuma gaza gurfanar da masu hannu a laifuka na ci gaba da tauye ’yancin addini tare da haifar da ramuwar gayya tsakanin al’ummomi.

A cewarta, wannan yanayi ne ke sa wasu daga cikin waɗanda rikice-rikice suka shafa ke kallon lamarin a matsayin tsanantawa ko ma abin da ya yi kama da kisan kare-dangi.

Kalaman nata sun zo ne bayan ce-ce-ku-cen da suka biyo bayan zargin da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi a baya cewa ana aiwatar da kisan kare-dangi kan Kiristoci a Najeriya.

Najeriya dai na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro da suka haɗa da ta’addanci a yankin Arewa, ayyukan masu garkuwa da mutane da ’yan bindiga, da kuma rikice-rikicen manoma da makiyaya a wasu sassan ƙasar.

Da aka tambaye ta ko bincikenta ya tabbatar da zargin kisan kare-dangi, Ghanea ta ce ta nemi ra’ayoyin masana shari’a kan batun.

Ta bayyana cewa duk da kasancewar wasu masana sun ce ba za a iya kawar da yiwuwar samun irin waɗannan laifuka a wasu wurare ba, ita ba ta ga wata hujja da ke nuna akwai wata manufa ko umarni kai tsaye daga gwamnati na hallaka wata al’umma bisa addini ko wata ƙabila ba.

Wakiliyar ta MDD ta ce za ta gabatar da cikakken rahotonta ga Hukumar Kare Haƙƙin Bil’adama ta Majalisar Ɗinkin Duniya a wani lokaci nan gaba domin ƙarin nazari da matakai.