Cutar Ebola cikin Yan kwanaki ta yi ajalin mutane sama da 200, tare da kama jimillar mutane sama da 900, a cikin ƙasashen gabashin Afrika musamman Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo.
Dr. Jean Kaseya shugaban na CDC ya ce jiran tallafin magunguna da rigakafi da kuma kayan kariya daga ƙetare na ɗaya daga cikin manyan dalilan da ke ƙara baiwa cutar damar bazuwa la’akari da irin tsahon lokacin da ake ɗauka kafin ƙasashen da ke bayar da tallafi su saki kuɗaden.
Lokaci yayi da ya kamata Afrika ta kula da kanta ba tare da jiran masu bayar da taimako ba.
Dr Jean ya bayar da misalin irin yadda ƙasashen Turai suka tashi haiƙan wajen magance cutar Corona cikin ƙanƙanin lokaci da samar da rigakafinta, duk da kasancewarta sabuwar cuta a duniya, amma irin hakan ta gagara samuwa a Afrika yankin da cutar Ebola ta shafe ɗimbin shekaru tana kisan al’umma.