Wani sabon bincike da aka gudanar a Isra’ila ya nuna cewa mafi yawan ‘yan ƙasar na ganin Iran ce ta fi cin moriyar rikicin Gabas ta Tsakiya da kuma yarjejeniyar da ta kulla da Amurka.


Binciken da jami’ar Hebrew ta Urushalima tare da cibiyar Agam suka gudanar tsakanin 17 zuwa 20 ga watan Yuni ya nuna cewa kashi 92 cikin 100 na waɗanda aka tambaya sun yi imanin cewa Iran ce ta yi nasara ko ta fi amfana da rikicin.


 kashi 83 cikin 100 sun ce tsaron Isra’ila na dogon lokaci ya raunana sakamakon rikicin.


Kazalika binciken ya nuna cewa kashi 72 cikin 100 na mahalarta ba su yarda da ikirarin Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, kan nasarorin da aka samu a yakin ba, yayin da fiye da rabin masu amsa tambayoyin suka bayyana yadda ya tafiyar da yakin a matsayin rashin nasara.


Haka, goyon bayan Netanyahu ya ragu daga kashi 40 cikin 100 a watan Maris zuwa kusan kashi 29 cikin 100 a watan Yuni.


Duk da haka, kusan rabin mahalarta binciken sun nuna goyon baya ga ci gaba da matakin soja kan kungiyar Hezbollah a Lebanon, ko da hakan zai iya janyo sabani da Amurka.


A gefe guda, ana sa ran ci gaba da tattaunawar mayar da yarjejeniyar Iran da Amurka ta zama ta dindindin a kasar Switzerland, duk da rikicin da ke ci gaba a Lebanon.