Dan majalisar dokokin Jihar Bauchi mai wakiltar mazabar Sakwa kuma Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar, Wanzam Zaki, ya rasu.
Wanzam ya rasu ne a safiyar ranar Lahadi a garin Bauchi bayan gajeriyar rashin lafiya.
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Abubakar Sulaiman, ne ya sanar da rasuwar cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mukhtar Garba Kobi, ya fitar a ranar Lahadi.
Kakakin Majalisar ya bayyana matuƙar alhininsa kan rasuwar, inda ya bayyana marigayin a matsayin jajirtaccen kuma sadaukararren mai hidimar jama'a wanda ya yi wa mazabarsa da Jihar Bauchi hidima ta gari da kwarewa.