Uwar gidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta taya iyaye maza a Najeriya da ma duniya baki ɗaya murnar Ranar Uba ta Duniya da ake gudanarwa a yau Lahadi.
A cikin saƙonta na murnar ranar, ta yaba da ƙoƙari, juriya da jajircewar iyaye maza wajen kula da tarbiyyar ’ya’yansu da kuma ɗaukar nauyin iyalansu.
Sanata Oluremi Tinubu ta bayyana cewa iyaye maza na taka muhimmiyar rawa wajen gina tunani, tarbiyya da ƙwarin gwiwar yara, lamarin da ke taimakawa wajen kyautata makomarsu.
Ta kuma ce soyayya, jagoranci, kariya da sadaukarwar da iyaye maza ke yi suna taimakawa wajen gina iyalai masu ƙarfi da al’ummomi nagari.
A cewarta, “A wannan Ranar Uba ta Duniya ta shekarar 2026, muna murnar soyayya, juriya da sadaukarwar da iyaye maza ke nunawa a faɗin Najeriya da ma duniya baki ɗaya.”