Hukumar Kula da Ayyukan tsaro na farar hula, Gidajen Gyaran Hali, Kashe Gobara da Shige da Fice (CDCFIB) ta karyata wata sanarwar bogi da ke yawo a kafafen sada zumunta wadda ke ikirarin cewa an dage aikin daukar ma’aikatan shekarar 2026.
Hukumar ta karyata Labarin ne cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X ranar Lahadi.
Hukumar ta bukaci masu neman aiki da daukacin jama’a da su yi watsi da takardar saboda ba ta da inganci.
Wannan na zuwa ne bayan hukumar ta saki sunayen wadanda suka samu nasara a jarabawar da hukumar ta gudanar da akayi da kwamfuta a watan nuwanbar 2025.
Inda hukumar ta bayyana cewa, wadan da suka samu nasarar zasu tafi mataki na gaba na daukar aikin, ciki har da ta gwajin lafiya da sauran gwaje-gwajen.
Gwaje-gwajen zasu shafi dukan masu neman guraben aiki a hukumar Kula da gidajen gyaran hali, da hukumar Kula da shige da fice ta kasa da kuma hukumar kashe gobara da hukumar Kula da tsaron farar hula ta civil defence