Wani rahoto da kafar yaɗa labarai ta Axios ta wallafa ya ce Amurka na neman Iran ta amince da bai wa masu binciken Majalisar Ɗinkin Duniya damar duba cibiyoyinta na nukiliya, a wani yunkuri na farfaɗo da tattaunawar da ke tsakanin ɓangarorin biyu.
Rahoton ya ambato wasu majiyoyi daga yankin da suka ce Washington na son a cimma yarjejeniya inda Iran za ta sake buɗe ƙofofin cibiyoyinta na nukiliya ga masu bincike na ƙasa da ƙasa.
An bayyana cewa wasu daga cikin waɗannan cibiyoyi sun taɓa fuskantar hare-hare daga Amurka da Isra’ila a baya, kuma ba a gudanar da irin wannan bincike ba tun watan Yunin shekarar 2025.
A cewar rahoton, a madadin wannan amincewa, Amurka na nazarin bai wa Iran damar amfani da wani ɓangare na kadarorinta da aka daskarar a ƙasashen waje, ciki har da asusun dala biliyan 6 da ke ƙasar Qatar.
Sai dai an ce za a takaita amfani da kuɗaɗen ne wajen sayen kayayyakin jin-ƙai kamar abinci, magunguna da sauran buƙatun yau da kullum, ba tare da amfani da su a wasu fannoni ba.
Rahoton ya kuma ce tattaunawar za ta mayar da hankali kan makomar shirin nukiliyar Iran da kuma ƙoƙarin samar da zaman lafiya da tsagaita wuta a yankin Gabas ta Tsakiya.
A gefe guda, ana nuna damuwa cewa rikicin da ke ci gaba da faruwa a Lebanon na iya kawo cikas ga ci gaban tattaunawar.
Mataimakin Shugaban Amurka, JD Vance, ya bayyana cewa tashin hankalin da ke yankin na iya yin tasiri ga ƙoƙarin diflomasiyyar da ake yi tsakanin ɓangarorin.
Ko da yake an samu yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hezbollah a baya-bayan nan, rahotanni na nuna cewa har yanzu akwai zarge-zargen karya yarjejeniyar da ke barazana ga dorewar zaman lafiya a yankin.