Mai neman takarar kujerar shugaban ƙasa a jam’iyyar PRP, Yakubu Kingsley, ya kalubalanci nasarar tsohon gwamnan Jihar Cross River, Donald Duke, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasar jam’iyyar a zaɓen shekarar 2027.
A cikin ƙarar da aka shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/1234/2026, Kingsley ta hannun lauyansa, D.A. Sulyman, ya shigar da ƙara a kan jam’iyyar PRP, Duke INEC a matsayin waɗanda ake ƙara na farko, na biyu da na uku bi da bi.
Mai ƙarar na neman kotu ta soke ayyana Duke a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, inda yake zargin cewa tsohon gwamnan ba cikakken ɗan jam’iyyar ba ne kuma bai da cikekken rajista.
Kingsley ya roƙi kotu ta tantance ko an ayyana Duke bisa ƙa’ida a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na PRP a zaɓen fidda gwani da aka gudanar ranar 25 ga Mayu, wanda aka sanar da sakamakonsa ranar 26 ga Mayu, duk da cewa ana zargin babu shi cikin rajistar mambobin jam’iyyar ba zuwa ranar 4 ga Mayu lokacin da aka miƙa kundin rajistar mambobin PRP ga INEC.
Haka kuma, ya yi tambaya kan ingancin ƙuri’un da aka kaɗa a zaɓen fidda gwanin a wasu jihohi, inda ya yi zargin cewa an samu kaɗa ƙuri’u fiye da adadin masu haƙƙin kaɗa kuri’a a wasu wurare.