Tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma tsohon sanata, Ahmed Mohammed Makarfi, ya yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya ayyana dokar ta-baci kan matsalar rashin tsaro a Najeriya.


Makarfi ya bayyana cewa halin da ƙasar ke ciki na rashin tsaro ya kai matakin da ke bukatar daukar matakin gaggawa domin dakile yawaitar hare-haren ‘yan bindiga, garkuwa da mutane da kuma kashe-kashen jama’a.



Akwai bukatar gwamnati ta ƙara ƙarfafa hukumomin tsaro, tare da samar musu da kayan aiki da dabarun zamani domin tunkarar matsalar cikin inganci.


Makarfi ya Kara da cewa, Najeriya na buƙatar haɗin kai tsakanin gwamnati da jama’a domin shawo kan matsalar tsaro da ta addabi sassa da dama na ƙasar.