Ma’aikatar Kula da Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Kano (KSPHCMB) ta amince da wasu muhimman matakai domin ƙarfafa ingancin ayyukan rigakafi, tabbatar da sahihancin bayanai da kuma inganta yadda ake gudanar da gangamin rigakafin BCU/IBRA na watan Yunin 2026.


An cimma waɗannan matsayai ne a taron kwanaki biyu na masu ruwa da tsaki da aka gudanar ƙarƙashin jagorancin Darakta Janar na ma’aikatar, Farfesa Salisu Ahmad Ibrahim, kamar yadda ke kunshe cikin wata sanarwar manema labarai da Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta KSPHCMB, Sa’adatu Sulaiman ANIPR, ta sanya wa hannu a ranar 21 ga Yunin 2026.


Bayan nazarin rahotannin da wakilai suka gabatar, taron ya amince da rusa gaba ɗaya tawagar masu gudanar da aikin rigakafi da aka tura Unguwar Hotoro ta Arewa da ke ƙaramar hukumar Nasarawa, tare da maye gurbinsu da sabbin ma’aikata cikin sa’o’i 24.


Haka kuma, an ba da umarnin dakatar da dukkan ma’aikatan da ke aiki a yankin nan take, ciki har da Jami’in Kula da Unguwa (WFP), wakilin WHO, wakilin SOLINA, wakilin UNICEF mai kula da unguwa, ma’aikatan Chigari da sauran jami’an da ke gudanar da ayyuka a yankin.


Taron ya kuma amince da dakatar da ayyukan gangamin rigakafi a Unguwar Hotoro ta Arewa a ranar Litinin, 22 ga Yunin 2026, domin bai wa sabbin ma’aikatan da za a tura damar samun horo da shiryawa kafin fara aiki.


A cewar sanarwar, za a ci gaba da gudanar da gangamin rigakafin a yankin daga ranar Talata, 23 ga Yunin 2026, yayin da kuma za a aika da takardun tuhuma (query) ga dukkan manyan masu sa ido na gwamnati da na abokan hulɗa da aka tura yankin domin bincike da ɗaukar matakan da suka dace.