Aliyu Muhammad ya bayyana alhininsa bayan da wasu fusatattun mutane suka kashe tare da ƙona matarsa, Ummulkhairi, a jihar Kaduna bisa zargin satar yara. Ya ce tun kwanaki biyu kafin faruwar lamarin yana jin gabansa na faɗuwa, amma bai gaya mata ba domin kada ta damu. A ranar da lamarin ya faru, sun yi sallama da safe yayin da matar ta tafi wani wa’azi, shi kuma ya tafi aiki. Daga baya aka sanar da shi cewa an kama matarsa da zargin satar yara kuma an kai ta gidan mai unguwa. Sai dai kafin a gudanar da bincike ko tabbatar da zargin, mutane sun taru a gidan suna neman a miƙa musu ita domin su hukunta ta. Lamarin ya jawo mutuwarta cikin wani yanayi mai tayar da hankali.