Lionel Messi, ya ƙara kafa wasu sabbin tarihi guda biyu a gasar cin Kofin Duniya bayan wasan rukuni na biyu da ƙasarsa ta buga da Austria a ranar Litinin.


Gwarzon dan wasan messi ya fara kafa tarihin da ba zai so a tuna da shi ba kafin daga bisani ya sake kafa wani sabon tarihi da ya ƙara tabbatar da matsayinsa a cikin manyan fitattun ‘yan wasan ƙwallon ƙafa na duniya.


Da farko, Messi ya zama ɗan wasan da ya fi kowa ɓarar da bugun daga kai sai mai tsaron raga a tarihin gasar Kofin Duniya ta FIFA.


Wannan ne karo na uku da Messi ya gaza cin fanareti a gasar Kofin Duniya, lamarin da ya sa ya zarce sauran ‘yan wasan da suka taɓa kafa irin wannan tarihin.


Lionel messi ya mayar da martani cikin salon da aka saba gani a wajensa, inda daga baya ya zura ƙwallo a ragar Austria, abin da ya sa ya zama ɗan wasan da ya fi kowa yawan cin ƙwallaye a tarihin gasar cin kofin duniya.


Da wannan ƙwallon ne Messi ya zarce tsohon ɗan wasan ƙasar Jamus Miroslav Klose wanda yake da jimullar ƙwallaye 17 da ya zura a raga kuma mafi yawa a tarihin gasar.


Haka kuma ya kafa tarihin zama mafi tsufa da ya ci ƙwallaye biyu a wasa guda na Kofin Duniya, inda ya karya tarihin da tsohon tauraron Kamaru Roger Milla ke riƙe da shi.


Kuma duk da cewa ɗaya daga cikin tarihin da ya kafa a ranar Litinin ba wanda zai so a tuna da shi ba ne, amma ya sake tunatar da duniya dalilin da ya sa mutane da dama ke kallonsa a matsayin mafi girman ɗan wasan ƙwallon ƙafa a zamaninsa.