Kungiyoyin Fulani a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya sun yi gargadin cewa zargin kabilar Fulani da hannu a ayyukan garkuwa da mutane ba tare da hujja ba na iya haifar da rikicin kabilanci da kuma dagula zaman lafiya a yankin.


Kungiyoyin sun bukaci Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Oyo da su gargadi mai fafutukar kare hakkin Yarabawa, Sunday Igboho, kan kalaman da suka ce na iya haddasa rashin jituwar kabilanci.


Wannan na zuwa ne bayan da Sunday Igboho ya bai wa masu garkuwa da mutane wa'adin sa'o'i biyu su sako wasu daliban da aka sace a Jihar Oyo, tare da yin barazanar daukar mataki idan ba a sake su ba.


A wata sanarwa da kungiyar Fulani ta fitar, ta ce abin damuwa ne yadda ake alakanta duk wani laifin garkuwa da mutane da Fulani, lamarin da ta ce na iya jefa rayukan Fulani mazauna yankin cikin hadari.


Kungiyar ta ce mafi yawan Fulani a yankin makiyaya ne da ke gudanar da harkokinsu cikin lumana, don haka bai dace a dora laifin wasu tsiraru kan daukacin al'umma ba.