Gwamnatin Jihar Kano ta rufe makarantun koyar da harkokin lafiya na IBN SINA College of Health Science and Technology da ke Dakata Kawaji kusa da Masallacin Juma’a, da kuma Life Line College of Health Science and Technology da ke Dakata Industrial Area, kan titin Bela Road, Tsamiyar Gare, tare da titin Mai Sikeli.


Wannann na cikin wata Sanarwa da Mai magana da yawun hukumar Nabilisi Abubakar Kofar na'isa ya sanyawa hannu.


Sanarwar ta bayyana cewa an ɗauki matakin rufe cibiyoyin ne bayan wani cikakken bincike da Ma’aikatar Lafiya ta gudanar, wanda ya nuna cewa cibiyoyin biyu ba su cika ƙa’idoji da mafi ƙarancin sharuddan da aka tanada domin kafawa da kuma gudanar da cibiyoyin koyar da harkokin lafiya a Jihar Kano ba.


A cewar ma’aikatar, cibiyoyin suna gudanar da ayyukansu ba tare da tantancewa da amincewar Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ba, sannan kuma ba su da sahalewa daga hukumomin ƙwararru da na sa ido da ke kula da ilimin lafiya da horar da ma’aikatan lafiya a Najeriya.


Binciken ya kuma gano manyan matsaloli da suka haɗa da ƙarancin ƙwararrun malamai, rashin ingantattun kayan koyarwa da wuraren koyo, ƙarancin ababen more rayuwa, da kuma gazawa wajen bin ƙa’idojin ilimi da gudanarwa da ake buƙata domin samar da ƙwararrun ma’aikatan lafiya yadda ya kamata.


Haka kuma, ma’aikatar ta lura da rashin bin ɗabi’un ƙwararru, ƙa’idojin hukumomin sa ido da sauran sharuddan da suka wajabbat da aka tanada domin tabbatar da ingancin ilimin lafiya da kuma ƙwarewar waɗanda za su zama ma’aikatan lafiya a nan gaba.


Da yake jawabi kan lamarin, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar Lafiya ya sake jaddada aniyar ma’aikatar na kare ɗalibai, iyaye da sauran al’umma daga cibiyoyin da ke tauye ingancin ilimi da ƙa’idojin ƙwarewa. Ya bayyana cewa horar da ma’aikatan lafiya dole ne ya kasance a cibiyoyin da suka cika ƙa’idojin da hukumomi suka amince da su.


Saboda haka, gwamnatin jihar ta yi gargaɗi ga masu gudanar da cibiyoyin koyar da harkokin lafiya a faɗin jihar da su tabbatar da cikakken bin dukkan dokoki da ƙa’idojin da suka shafi ayyukansu. Ta ce rufe cibiyoyin da ba su cika sharudda ba wani muhimmin mataki ne na tabbatar da ingantaccen ilimin lafiya, kare muradun ɗalibai, da kuma ci gaba da ɗaukaka nagartar ayyukan kiwon lafiya a faɗin Jihar Kano.