Rundunar yansanda na shirin fara amfani da na’urorin daukar hoto da bidiyo da jami’ai za su rika sanyawa a jikinsu yayin aiki, domin tabbatar da gaskiya, rikon amana da kuma inganta hulda tsakanin jami’an tsaro da al’umma.


Mataimakin babban sufeton yansanda mai kula da sashen horaswa da ci gaba, DIG Frank Mba, ne ya bayyana hakan, inda ya ce shirin na daga cikin matakan da rundunar ke dauka wajen zamanantar da aikin yansanda da kuma kara amincewar jama’a ga hukumar.


A cewarsa, amfani da wadannan na’urori zai taimaka wajen rage zarge-zargen cin zarafi, tabbatar da adalci yayin gudanar da aiki da kuma samar da sahihan hujjoji idan aka samu sabani ko korafi tsakanin jami’an tsaro da jama’a.


Ya kara da cewa a wannan zamani, nasarar aikin tsaro ba ta tsaya ga kama masu laifi kawai ba, har ma da yadda jami’an tsaro ke gudanar da aikinsu cikin gaskiya da nuna kwarewa, abin da zai kara karfafa amincewar jama’a ga rundunar.


Shirin na daga cikin gyare-gyare da sauye-sauyen da rundunar yansandan Najeriya ke ci gaba da aiwatarwa domin inganta ayyukanta, kara kwarewar jami’ai da kuma tabbatar da cewa an gudanar da aikin tsaro cikin gaskiya da adalci.