Wani abun fashewa ya tashi a wani sashe na kasuwar Mushin da ke jihar Lagos, inda mutum guda ya jikkata bayan wata mota ta tarwatse sakamakon fashewar. Lamarin ya faru ne da tsakar dare a yankin Oke Mushin, cikin kasuwar sayar da takalma.

Rahotanni sun nuna cewa ana zargin an dasa wani abun fashewa (IED) a ƙarƙashin motar, wanda ya fashe lokacin da aka kunna injinta. Kwamishinan 'yan sandan jihar Lagos, ya ce jami'an kwance abubuwan fashewa sun isa wurin nan take, kuma binciken farko ya tabbatar da cewa an sanya abun fashewar ne a ƙarƙashin motar a gefen fasinja.

Ana ci gaba da bincike domin gano mamallakin motar da kuma musabbabin lamarin.