Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation Hadin Kai sun ceto mutum 47, mafi yawansu mata da ƙananan yara, daga hannun mayaƙan ISWAP a yankin Kangarwa da ke ƙaramar hukumar Kukawa ta jihar Borno.

A cewar rundunar, an samu nasarar ceton mutanen ne a ranar 20 ga Yuni, 2026 bayan wani samame da sojoji suka kai, wanda ya tilasta wa ‘yan ta’addar tserewa tare da barin waɗanda suka tsare.

Sanarwar ta ce hare-haren ƙasa da na sama da aka kai wa sansanonin ISWAP a yankin Tafkin Chadi sun haddasa rikicewa a tsakanin ‘yan ta’addar, lamarin da ya bai wa waɗanda aka tsare damar samun ‘yanci bayan sun shafe lokaci mai tsawo a hannunsu.

An kai mutanen da aka ceto wuraren tsaro domin samun kulawar lafiya da tallafin jin kai, yayin da rundunar ta tabbatar da ci gaba da kai farmaki kan ‘yan ta’adda domin dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas.