Mai martaba Sarkin Kano Muhammad Sunusi II ya yi kira ga al'ummar jihar Kano da su dasa bishiyu a muhallan su domin inganta muhalli.
Sarkin ya yi wannan kiran ne lokacin da ya karbi bakuncin kwamishinan ruwa muhalli da sauyin yanayi Dakta Tahir Muhammad Hashim a fadar sa domin kaddamar da aikin dashen bishiyu a fadin jihar ban.
Da yake jawabi Mai martaba Sarki ya yaba wa kwamishinan bisa kaddamar da wannan aiki mai muhimmanci na inganta muhalli, tare da godiya bisa gudunmawar bishiyu 500 da aka kawo masa.
A nasa jawabin kwamishinan ruwa muhalli da sauyin yanayi na jihar Kano Dakta Tahir Muhammad Hashim ya bayyana cewa aikin dashen bishiyun wani bangare ne na cika umarnin gwamna Abba Kabir Yusuf na dasa bishiyu miliyan 10 a fadin jihar nan.