Sanata mai wakiltar Kebbi ta Kudu, Garba Maidoki, ya sauya sheƙa daga jam’iyyar APC zuwa ADC, inda ya danganta matakin da rikice-rikicen cikin gida da kuma zargin rashin adalci a zaɓen fidda gwani da aka gudanar a jihar Kebbi.

An karanta wasiƙar ficewarsa a zauren Majalisar Dattawa a ranar Talata ta hannun Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin. A cikin wasiƙar, Sanata Maidoki ya ce rikice-rikicen da ke addabar APC sun shafi harkokinsa na siyasa, kuma ya zaɓi ADC ne saboda manufofinta da yake ganin za su fi amfani ga al’ummarsa da ƙasa baki ɗaya.

Ya kuma zargi APC da gazawa wajen tabbatar da adalci, zaman lafiya da haɗin kai, musamman a zaɓen fidda gwani da aka gudanar a jihar Kebbi. Sai dai Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya musanta cewa APC na fama da rikici, tare da bayyana shirinsa na shiga tsakani domin sasanta duk wata matsala da ka iya kasancewa.