Shugabar Hukumar UNAIDS ta Majalisar Ɗinkin Duniya, Winnie Byanyima, ta yi gargaɗin cewa janye tallafin yaƙi da cutar HIV da Amurka ta yi wa Afirka ta Kudu na iya haifar da asarar rayuka da kuma jefa masu ɗauke da cutar cikin mawuyacin hali.

Ta bayyana hakan ne gabanin taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan cutar HIV, inda ta ce tallafin Amurka ya taka muhimmiyar rawa musamman wajen shirye-shiryen hana yaɗuwar cutar a ƙasar.

Rahotanni sun nuna cewa jami'an Amurka sun danganta matakin da zargin rashin kare haƙƙin fararen fata a Afirka ta Kudu, zargin da gwamnatin Pretoria ta musanta. A nata ɓangaren, Ma'aikatar Lafiya ta Afirka ta Kudu ta ce duk da rashin samun sanarwa a hukumance, ta daɗe tana shirye-shiryen dogaro da kai wajen gudanar da shirye-shiryen yaƙi da cutar HIV.