Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa ana amfani da cin zarafi na jima'i a matsayin makamin yaƙi a rikicin Sudan, inda ta ce adadin lokutan da aka tabbatar sun kasance kaɗan ne idan aka kwatanta da ainihin yawan laifukan da ake aikatawa.

A wani rahoto da Ofishin Kare Haƙƙin Dan Adam na Majalisar Ɗinkin Duniya ya fitar, an ce an samu rahotannin lokuta 546 na cin zarafi masu alaƙa da rikici a jihohi 16 daga cikin 18 na Sudan tsakanin watan Afrilun 2023 da Afrilun 2026.

Rahoton ya nuna cewa aƙalla mutum 838 ne abin ya shafa, ciki har da mata 539, yara mata 284, maza takwas da yara maza bakwai. MDD ta ce irin waɗannan laifuka na ƙaruwa ne yayin da rikicin ke yaɗuwa zuwa sabbin yankuna da kuma hanyoyin da masu gudun hijira ke bi.

Hukumar ta ƙara da cewa ana amfani da cin zarafin ne wajen tsoratar da fararen hula da kuma haddasa musu mummunan raɗaɗin tunani a yankunan da rikicin ya shafa.