Kamfanin Matatar Mai ta Dangote Petroleum Refinery ya yi watsi da zarge-zargen da ke cewa ana fitar da kayayyakin man fetur da ake tacewa a matatar zuwa birnin Lomé na ƙasar Togo, sannan daga baya a sake shigo da su Najeriya.
PUNCH Online ta rawaito cewa wasu bayanai da suka yadu a kafafen sada zumunta sun yi ikirarin cewa ana fitar da kayayyakin da matatar Dangote ke samarwa zuwa ƙasashen maƙwabta kafin a dawo da su Najeriya.
A wata sanarwa da kamfanin ya fitar ta shafinsa na X ranar Talata, mahukuntan matatar sun bayyana zargin a matsayin marar tushe kuma wanda bai dogara da haƙiƙanin kasuwanci ba.
Mahukuntan sun ce sun ga ya zama dole su mayar da martani kan batun duk da manufarsu ta kaucewa mayar da martani ga abin da suka kira “zarge-zarge marasa tushe da hujja.”
A cewar kamfanin, zargin bai yi daidai da bayanan da ake da su kan harkokin cinikayya, ƙa’idodin kasuwanci, ko manufofin kasuwancin kamfanin ba.
“Bisa tsarinmu, ba ma mayar da martani ga zarge-zarge marasa tushe da hujja, kasancewar hankalinmu da ƙudurimmu a yanzu sun karkata ne wajen tabbatar da wadatar makamashi a Najeriya da ma nahiyar Afirka baki ɗaya.”