Faransa ta sanar da tabbatar da ɓullar cutar Ebola a ƙasar bayan wani likita da ya dawo daga aikin jin ƙai a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo (DR Congo) ya kamu da cutar.

Ma’aikatar Lafiya ta Faransa ta ce an kwantar da likitan a wani asibiti na musamman domin kula da shi, kuma a halin yanzu yana cikin yanayi mai kyau.

Rahotanni sun nuna cewa wannan ne karo na farko da aka tabbatar da kamuwar cutar Ebola a Faransa, yayin da hukumomi suka fara bin diddigin duk mutanen da suka yi hulɗa da marar lafiyar domin hana yaɗuwar cutar.

A lokaci guda, Uganda da DR Congo na ci gaba da fama da ɓarkewar cutar, inda aka samu dubban masu kamuwa da ita da kuma ɗaruruwan mace-mace. Sai dai hukumomin Faransa sun tabbatar wa jama'a cewa babu wani babban haɗarin yaɗuwar cutar a cikin al'umma, tare da ɗaukar matakan kariya da suka dace.