Rundunar Ƴansandan Jihar Kaduna ta sanar da cewa jami'anta sun yi nasarar ceto mutum tara da aka yi garkuwa da su a Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari da ke jihar.
Sai dai rundunar ta bayyana cewa wasu jami'anta biyu sun rasa rayukansu bayan da ƴanbindiga suka yi musu kwanton ɓauna a lokacin da suke dawowa daga aikin ceton mutanen.
A wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ya ce lamarin ya faru ne a ranar 24 ga Yuni, 2026, bayan samun sahihan bayanan sirri kan wasu ƴanbindiga kusan 15 ɗauke da makamai da suka kai hari ƙauyen Unguwan Sa'idu da ke kusa da Birnin Gwari.
Sanarwar ta ce maharan sun yi garkuwa da wasu manoma yayin da suke aiki a gonakinsu. Bayan samun rahoton, jami'an ƴansanda tare da haɗin gwiwar ƴan banga suka bi sawun maharan tare da yin artabu da su.
Sakamakon musayar wutar da aka yi, ƴanbindigan sun tsere zuwa cikin daji a kan babura, inda suka bar mutum tara da suka yi garkuwa da su, waɗanda jami'an tsaro suka ceto cikin nasara.
Sai dai a yayin da jami'an ke komawa daga aikin, maharan sun sake shirya kwanton ɓauna, inda suka buɗe musu wuta tare da harbin jami'ai biyu. An garzaya da su asibiti, amma daga bisani likitoci suka tabbatar da rasuwarsu.
Rundunar ƴansandan ta jajanta wa iyalan jami'an da suka rasu tare da jaddada ƙudurinta na ci gaba da yaƙi da miyagun laifuka da tabbatar da tsaro a faɗin jihar.