Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da kafa wani kwamiti na musamman domin ƙarfafa yaƙi da shaye-shaye da safarar miyagun ƙwayoyi a faɗin jihar.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, an bayyana cewa matakin ya biyo bayan yadda matsalar miyagun ƙwayoyi ke ci gaba da barazana ga rayuwar matasa da zaman lafiyar al’umma.

Sanarwar ta ce kwamitin zai mayar da hankali wajen gano manyan wuraren da ake safara da sayar da miyagun ƙwayoyi, tare da haɗa kai da hukumomin tsaro domin kai samame da cafke masu hannu a harkar.

Haka kuma, an ɗora wa kwamitin alhakin tattara bayanan sirri, musayar bayanai tsakanin hukumomin tsaro, gano hanyoyin da ake amfani da su wajen safarar miyagun ƙwayoyi, da kuma wayar da kan jama’a kan muhimmancin kai rahoton duk wani aiki da ake zargin yana da alaƙa da miyagun ƙwayoyi ko wasu ayyukan ɓata-gari.

Bugu da ƙari, kwamitin zai yi aiki kafaɗa da kafaɗa da ɓangaren shari’a domin tabbatar da gaggauta gurfanar da waɗanda ake zargi da aikata laifukan da suka shafi miyagun ƙwayoyi tare da tabbatar da hukunta masu laifi.

Tsohon shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-Ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimingado, ne zai jagoranci kwamitin.

Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da wakilai daga hukumomin tsaro da suka haɗa da NDLEA, DSS, Rundunar ’Yan Sanda, NSCDC da Hukumar Kwastam, tare da wakilai daga ma’aikatun gwamnati, sarakunan gargajiya, malamai da kuma ƙungiyoyin farar hula.