Akalla mutum 10 ne aka ceto da ransu bayan wani ginin bene ya rufta a jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya.
Lamarin ya faru ne a kan titin Old Ojo Road, kusa da tashar motar Alakija da ke kan babbar hanyar Legas zuwa Badagry. Rahotanni sun nuna cewa jami'an agajin gaggawa na ci gaba da aikin bincike domin tabbatar da ko akwai wasu da suka maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan ginin.
A cewar Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Legas, an samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 11:37 na safe, lamarin da ya sa aka tura jami'an ceto zuwa wurin cikin gaggawa.
Babbar Daraktar Hukumar, Margaret Adeseye, ta tabbatar da cewa an yi nasarar ceto mutum 10 daga cikin ɓaraguzan ginin.
Ta bayyana cewa waɗanda aka ceto sun samu raunuka daban-daban, kuma an garzaya da su asibiti domin samun kulawar likitoci.
Margaret Adeseye ta ƙara da cewa ana ci gaba da aikin ceto da bincike a wurin domin tabbatar da ko akwai wasu da har yanzu suke ƙarƙashin ginin da ya rufta.
A halin yanzu, hukumomi ba su bayyana musabbabin ruftawar ginin ba, sai dai sun ce za a gudanar da cikakken bincike bayan kammala aikin ceto.