Cibiyar Gyaran Hali ta Kiru a Jihar Kano ta yi kira ga iyaye, shugabannin al’umma, malamai da sauran masu ruwa da tsaki da su haɗa kai wajen kare matasa daga illolin shan miyagun ƙwayoyi, yayin da ake bikin Ranar Yaƙi da Shan Miyagun Ƙwayoyi da Fataucinsu ta Duniya a yau.
A cikin wata sanarwa da cibiyar ta fitar, ta ce tana haɗa kai da ƙasashen duniya wajen sabunta ƙudirin hana shan miyagun ƙwayoyi, gyaran rayuwar masu fama da matsalar da kuma gina al’umma mai lafiya da tsaro.
Sanarwar ta bayyana cewa shan miyagun ƙwayoyi na daga cikin manyan barazanar da ke fuskantar matasa, iyalai da al’umma, domin yana lalata makoma, yana haddasa matsalolin lafiyar jiki da ta ƙwaƙwalwa, yana ƙara aikata laifuka tare da kawo cikas ga ci gaban ƙasa.
Cibiyar ta ce tana ci gaba da jajircewa wajen dawo da fata da sake gina rayuwar masu fama da shaye-shaye ta hanyar ba su kulawa ta ƙwararru, shawarwari, gyaran hali da kuma taimaka musu su koma cikin al’umma.