Babbar kotun tarayya da ke Lokoja ta soke wani hukuncin da ta yanke a baya wanda ya umarci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta yi wa jam'iyyar NDC rajista a matsayin jam'iyyar siyasa.

Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa alƙalin kotun, Mai Shari'a Isah Dashen, ne ya yanke sabon hukuncin a yau Juma’a.

Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci INEC ta yi wa jam'iyyar CDA rajista.

A waccan shari'ar, Mai Shari'a Obiora Egwuatu ya umarci INEC da ta bai wa jam'iyyar CDA takardar rajista cikin kwanaki bakwai, bayan yanke hukunci kan ƙarar da Tamunotonye Samuel Solomon Inioribo da wasu mutum biyu suka shigar.