Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da kakkaɓe masu safarar miyagun ƙwayoyi da kuma masu ta'ammali da su a faɗin Najeriya.
Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a a Abuja, yayin taron ƙarƙare bukukuwan Ranar Yaƙi da Shan da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Duniya, wanda Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta shirya.
A wata sanarwa da mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar, an ce Shugaba Tinubu ya samu wakilcin Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi (SAN).

A cewarsa, gwamnati ta himmatu wajen samar wa matasa ingantacciyar rayuwa da damammakin da za su ba su kyakkyawar makoma, wanda hakan ne ya sa ta ke ci gaba da ɗaukar matakai masu tsauri wajen yaƙi da matsalar miyagun ƙwayoyi.
Shugaban ya kuma yaba da ƙoƙarin jami'an NDLEA, musamman wajen cafke masu safarar miyagun ƙwayoyi da kuma ƙwace tarin ƙwayoyin da ake safararsu a cikin gida da wajen Najeriya.
A nasa jawabin, Shugaban Hukumar NDLEA, Janar Buba Marwa mai ritaya, ya yabawa jajircewar jami'an hukumar, inda ya bayyana cewa sun yi nasarar ƙwace miyagun ƙwayoyi masu nauyin kilogram miliyan 5.3, waɗanda darajarsu ta haura naira tiriliyan 1.5, cikin watanni 18 da suka gabata.