Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kaduna ta sanar da gurfanar da wasu ƙarin mutum 17 da ake zargi da hannu a kisan gilla da aka yi wa wata mata a Unguwar Maraban Jos a makon da ya gabata.
A cikin wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar, an bayyana cewa an gurfanar da waɗanda ake zargin ne yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
Sanarwar ta ce bayan kammala binciken farko, adadin mutanen da aka gurfanar ya kai 33, inda ake tuhumarsu da laifukan haɗa baki da kuma gudanar da taro ba bisa ƙa'ida ba.
Rundunar ta kuma bayyana cewa mutum 30 da aka kama bayan aukuwar lamarin ba a samu wata shaida da ke nuna suna da hannu a aikata laifin ba, saboda haka an sake su ba tare da wani sharaɗi ba.
'Yan sandan sun tabbatar da cewa bincike kan lamarin na ci gaba, tare da jaddada aniyarsu ta gano da kuma kamo duk wanda ake zargi da hannu kai tsaye ko a kaikaice wajen aikata wannan laifi domin ya fuskanci hukunci bisa doka.:::