Gwamnatin Jihar Kebbi ta yi watsi da rahoton da ƙungiyar **Médecins Sans Frontières (MSF) ta fitar, wanda ya yi iƙirarin cewa ana samun mace-macen ƙananan yara sakamakon matsananciyar tamowa a jihar.


Rahoton na MSF ya nuna damuwa kan ƙarin yawan yara masu fama da rashin abinci mai gina jiki, inda ya ambaci wasu alkaluman da aka danganta da UNICEF da ke nuna cewa kusan yara 30 cikin 100 masu ƙasa da shekara biyar na mutuwa a kowace rana sakamakon tamowa, tare da cewa kusan rabin waɗannan mace-macen na faruwa ne a Jihar Kebbi.


Sai dai, Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kebbi, Yakubu Ahmed, ya bayyana wa BBC cewa gwamnatin jihar ba ta amince da sahihancin waɗannan alkaluma ba.


Ya ce gwamnatin na ƙalubalantar rahoton, tare da buƙatar MSF da UNICEF su gabatar da hujjoji da za su tabbatar da ikirarin da suka yi.


A cewarsa, idan da irin waɗannan mace-mace na faruwa a faɗin jihar, da gwamnati ta kasance cikin waɗanda suka fara samun labarin hakan.


"Gaskiya muna ƙalubalantar wannan ƙididdiga da suka bayar. Idan irin wannan abu na faruwa, ya kamata gwamnati ta fara sani. A ce yara na mutuwa da yawa a kowace rana ba tare da gwamnatin jihar ta sani ba, abin mamaki ne," in ji kwamishinan.


Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar na buƙatar ko dai MSF da UNICEF su gabatar da gamsassun hujjoji da ke tabbatar da rahoton, ko kuma su janye ikirarinsu tare da ba da haƙuri idan ba za su iya tabbatar da shi ba.


Rahoton ya ƙara jawo muhawara kan halin da ake ciki game da matsalar tamowa a jihar, yayin da gwamnatin Kebbi ke ci gaba da musanta sahihancin bayanan da aka fitar.