Manchester City ta cimma yarjejeniya da Nottingham Forest domin ɗaukar ɗan wasan tsakiya na Ingila, Elliot Anderson, kan kuɗin fam miliyan 116, wanda zai zama mafi tsadar ciniki a tarihin ƙungiyar idan aka kammala yarjejeniyar.
Ana sa ran Anderson mai shekara 23 zai yi gwajin lafiyarsa nan ba da jimawa ba kafin ya sanya hannu kan kwantiraginsa da zakarun Premier League a filin wasa na Etihad.
Majiyoyi daga Manchester City sun tabbatar da cewa yarjejeniyar ta kai fam miliyan 116 ba tare da wani ƙarin kuɗin da zai danganci cika wasu sharuɗɗa ba.
Sai dai wasu rahotanni sun ce jimillar kuɗin cinikin na iya kai wa fam miliyan 130 idan aka haɗa da wasu ƙarin kuɗaɗen da suka danganci nasarori, lamarin da zai sa ya zama mafi tsadar ciniki a tarihin ƙwallon ƙafa na Birtaniya.
Rahotanni sun nuna cewa Nottingham Forest ta ƙi tayi biyu da Manchester City ta fara gabatarwa, kafin daga bisani ta amince da tayi na uku.
Ana sa ran Forest za ta yi amfani da wani ɓangare na kuɗin cinikin wajen ƙarfafa tawagarta, inda ake alaƙanta ta da sayen Lucas Bergvall daga Tottenham da kuma Davide Frattesi daga Inter Milan.
A halin yanzu, Anderson na tare da tawagar Ingila a gasar cin Kofin Duniya, kuma ana sa ran zai buga wasan ƙarshe na matakin rukuni da Panama a ranar Asabar. A wata hira da BBC Sport, ɗan wasan ya bayyana cewa ya ajiye batun makomarsa a matakin kulob har sai bayan kammala gasar.:::