Ana shirin yin gwanjon ƙwallon da fitaccen ɗan wasan Argentina, Diego Maradona, ya ci Ingila da ita a gasar cin Kofin Duniya ta 1986, inda za a fara sayar da ita daga dala miliyan 2.5, a cewar kamfanin Heritage Auctions.

Kamfanin ya bayyana ƙwallon a matsayin ɗaya daga cikin mafi muhimmanci kuma mafi darajar kayayyakin tarihin ƙwallon ƙafa da za a taɓa sayarwa.

Rahotanni sun nuna cewa ana sa ran ƙwallon za ta iya zarce dala miliyan 9.2 da aka biya a shekarar 2022 domin sayen rigar da Maradona ya saka a wasan da Argentina ta doke Ingila a gasar Kofin Duniya ta 1986.

Ɗaya daga cikin ƙwararrun masu shirya gwanjo a Heritage Auctions, Mike Provenzale, ya ce yana da wahala a hasashen adadin kuɗin da ƙwallon za ta kai, domin babu wani irin kayan tarihi makamancinta da aka taɓa sayarwa.

Za a gudanar da gwanjon ne a lokacin da kasuwar kayayyakin tarihin wasanni, musamman na ƙwallon ƙafa, ke ci gaba da bunƙasa, abin da masana suka danganta da ƙarin sha'awar da Gasar Cin Kofin Duniya ta FIFA ta 2026, da ake karɓar bakuncinta a Amurka, Canada da Mexico, ta haifar.

Provenzale ya ce Amurka ce ke jagorantar kasuwar kayayyakin tarihin wasanni a duniya, inda ya bayyana cewa masu tara irin waɗannan kayayyaki na ƙara yawa, lamarin da ke ci gaba da ɗaga darajarsu a kasuwa.