Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya rantsar da sabbin kwamishinoni na Hukumar Tara Kuɗaɗen Shiga da Rabon Arzikin Ƙasa (RMAFC) da kuma Hukumar Ƙidayar Jama’a ta Ƙasa (NPC).

An gudanar da bikin rantsarwar ne a ranar Litinin, kafin fara zaman Majalisar Zartarwa ta Tarayya (Federal Executive Council – FEC) da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Daga cikin waɗanda aka rantsar a matsayin kwamishinonin RMAFC akwai tsohon shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), Abdullahi Mukhtar Mohammed, mai wakiltar Jihar Kaduna, da kuma Amina Gamawa, mai wakiltar Jihar Bauchi.

Haka kuma, Shugaba Tinubu ya rantsar da sabbin kwamishinoni shida na Hukumar Ƙidayar Jama’a ta Ƙasa (NPC). Su ne:

  • Kolawole Oladipupo Alabi – Jihar Ekiti
  • Nasiru Mu’azu – Jihar Zamfara
  • Isaka Alada Yahaya – Jihar Kwara
  • Farfesa Sadiq Isah Radda – Jihar Katsina
  • Suleiman Umar – Jihar Jigawa
  • Chiso Abdullahi Dattijo – Jihar Sokoto.

Ana sa ran sabbin kwamishinonin za su taka muhimmiyar rawa wajen inganta ayyukan hukumomin da suke jagoranta, musamman a fannonin ƙidayar jama’a, tattara bayanai da kuma rabon kuɗaɗen shiga na ƙasa.