Babbar Kotun Tarayya ta ƙaddamar da sabbin ka'idojin gudanar da shari'o'in gabanin zaɓe domin hanzarta shari'a, tabbatar da adalci da rage jinkirin sauraron ƙorafe-ƙorafe.
Sabbin ka'idojin, waɗanda Babban Alƙalin Kotun Tarayya, Mai Shari'a John Tsoho, ya amince da su, sun fara aiki a dukkan rassan kotun a faɗin ƙasar.
Daga cikin muhimman sauye-sauyen akwai buɗe ma'aikatun rajistar kotu a ranakun Asabar, Lahadi da hutun gwamnati domin karɓar takardun shari'o'in da suka shafi zaɓe, tare da ba kotu damar amfani da imel da sauran hanyoyin sadarwa na zamani wajen isar da sanarwa cikin gaggawa.
Haka kuma, sabbin ka'idojin sun tanadi matakan rage jinkirin shari'a, inda aka kayyade cewa ba za a amince da yawan neman dage zaman kotu ba sai idan akwai dalilai da doka ta amince da su.