Kotun Babbar Jihar Kaduna ta yi watsi da bukatar beli da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya gabatar a ranar Litinin, a shari'ar da ake masa kan tuhume-tuhume guda tara da suka shafi zargin amfani da mukami ba bisa ka'ida ba.


Yayin yanke hukunci kan bukatar, alkalin kotun, Mai Shari'a Diruis Khobo, ya bayyana cewa bukatar ba ta da inganci, kuma isassun hujjoji masu gamsarwa da za su tabbatar da cancantarsa ta samun beli ba.


Alkalin ya ce mai neman belin bai gabatar da sahihan hujjoji ko takardun da za su iya gamsar da kotu ta yi amfani da ikon da take da shi wajen amincewa da bukatarsa ba.


An gudanar da zaman kotun ba tare da halartar wanda ake tuhuma ba, domin har yanzu yana tsare a hannun Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka Masu Alaka (ICPC).


Duk da kin amincewa da bukatar belin, Mai Shari'a Khobo ya umarci ICPC da ta bai wa El-Rufai damar ganin tawagar likitocinsa ko kuma zuwa duk wata cibiyar lafiya da ya zaɓa a cikin Najeriya domin samun kulawar lafiya da ta dace.


Kotun ta kuma umarci cewa tsohon gwamnan ya ci gaba da kasancewa a tsare a hannun hukumar yaki da cin hanci da rashawa har sai an kammala sauraron shari'ar.