Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da soke lasisin aiki na bankunan microfinance 46, matakin da ya fara aiki daga 1 ga Yulin 2026.
CBN ta ce an ɗauki matakin ne saboda bankunan da abin ya shafa sun gaza cika muhimman ƙa'idojin da ake buƙata domin ci gaba da gudanar da harkokin banki.
A cewar bankin, daga cikin dalilan da suka jawo soke lasisin akwai rashin isassun kadarori don biyan basussuka, dakatar da ayyuka ba tare da amincewar hukuma ba, rashin gudanar da harkokin banki na dogon lokaci, gaza fara aiki cikin wa'adin da aka tanada, da kuma kasa cika mafi ƙarancin jarin da doka ta tanada.
CBN ta bayyana cewa matakin na daga cikin ƙoƙarinta na kare masu ajiya, tabbatar da bin ƙa'idojin banki da kuma ƙarfafa tsarin kuɗi na ƙasar.
Bankunan da aka soke lasisinsu sun haɗa da:
- Minji-Se Churchill MFB (Rivers)
- Merchant MFB (Abia)
- Janmaa MFB (Kwara)
- Busu MFB (Niger)
- Gold MFB (Lagos)
- Zain MFB (Kano)
- Bompai MFB (Kano)
- Ajwa MFB (Kano)
- NOW NOW Digital MFB (Kano)
- Crystabel Microfinance Bank (Bayelsa)
- Chanelle MFB (Lagos)
- Abia SME MFB (Abia)
- Kamba MFB (Kebbi)
- Iwade MFB (Ogun)
- Winview MFB (Abuja)
- Zuru MFB (Kebbi)
- Minjibir MFB (Kano)
- Shanono MFB (Kano)
- Sumaila MFB (Kano)
- Rimin Gado MFB (Kano)
- Mwaghavul MFB (Plateau)
- Sycamore MFB (Kano)
- Tofa MFB (Kano)
- Safegate MFB (Lagos)
- Creekline MFB (Delta)
- Bestar MFB (Oyo)
- Livingspring MFB (Cross River)
- Apple MFB (Ogun)
- Stanford MFB (Akwa Ibom)
- Frontline MFB (Anambra)
- Zafec MFB (Kaduna)
- Supreme MFB (Lagos)
- Bejin-Doko MFB (Niger)
- Kanopoly MFB (Kano)
- Bellbank MFB (Kano)
- Yeneng MFB (Plateau)
- Creditville MFB (Lagos)
- MBAG MFB (Lagos)
- Straight Sahara MFB (Benue)
- OurPass MFB (Ondo)
- Verdant MFB (Lagos)
- Basawa MFB (Kaduna)
- Casha MFB (Abuja)
- Esteem MFB (Kano)
- Entrepreneur MFB (Lagos)
- Avantus MFB (Osun)