Shugaban ƙasar China, Xi Jinping, ya yi alƙawarin ci gaba da ƙarfafa da zamanantar da rundunar sojin ƙasar, tare da ƙara kaimi wajen yaƙi da cin hanci da rashawa a cikin Jam'iyyar Kwaminis ta China (CCP).

Xi ya bayyana hakan ne yayin bikin cika shekaru 105 da kafuwar Jam'iyyar Kwaminis ta China, inda ya yi jawabi ga manyan jami'an gwamnati, shugabannin jam'iyya da hafsoshin soji.

Ya ce ƙarfafa rundunar soji na daga cikin manyan manufofin gwamnatin China, tare da jaddada cewa yaƙi da cin hanci zai ci gaba domin tabbatar da ingancin shugabanci.

Jam'iyyar Kwaminis ta China an kafa ta ne a 1 ga Yulin 1921, kuma tana da sama da mambobi miliyan 101 a ƙarshen shekarar da ta gabata.

Xi ya kuma sake nanata matsayar Beijing kan Taiwan, yana mai cewa China ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare abin da ta ke kira cikakken ikon ƙasarta.

Haka kuma, ya yi kira ga al'ummar China da su kasance cikin shiri da haɗin kai, tare da gargadin kada su amince da duk wani katsalandan daga ƙasashen waje, ko da yake bai ambaci wata ƙasa da suna ba.