Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ta hannun Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, ya ƙaddamar da aikin Sashe na Farko na Babbar Hanyar Akwanga–Jos–Bauchi–Gombe–Yobe–Maiduguri Super Highway a garin Akwanga da ke Jihar Nasarawa.
Sashen farko na aikin ya ƙunshi titin Akwanga zuwa Jos mai tsawon kilomita 125, kuma an ƙaddamar da shi ranar Laraba.
Aikin yana ƙarƙashin kulawar Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi, a matsayin wani ɓangare na shirin Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa da inganta manyan hanyoyin ƙasa domin ƙarfafa haɗin kai tsakanin jihohi da kuma bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa.
Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da aikin, Sanata David Umahi ya bayyana cewa babbar hanyar mai tsawon kusan kilomita 700 za a aiwatar da ita a matakai daban-daban.
Ya ce idan aka kammala aikin, zai sauƙaƙa zirga-zirga, inganta safarar kayayyaki da fasinjoji, ƙarfafa harkokin kasuwanci, tare da hanzarta ci gaban tattalin arziƙi a jihohin Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Gabas.