Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta Najeriya (DSS) ta gurfanar da wasu mutum biyar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bisa zarginsu da ɓoye bayanai kan inda tsohon gwamnan Jihar Bayelsa kuma tsohon ƙaramin ministan albarkatun man fetur, Timipre Sylva, yake.
A cewar DSS, ana zargin waɗanda ake tuhuma da haɗa baki wajen ɓoye inda Mista Sylva yake, wanda hukumar ta ce mutum ne da hukumomin tsaro ke nema.
Dukkan waɗanda ake tuhuma sun musanta zarge-zargen da aka karanta musu a gaban kotu.
Lauyan DSS, Emmanuel Orubor, ya roƙi kotun ta sanya ranar fara sauraron shari'ar domin gabatar da shaidu. A nasa ɓangaren, lauyan wasu daga cikin waɗanda ake tuhuma, Sanusi Musa (SAN), ya nemi kotun ta ba su beli.
Mai shari'a Peter Lifu ya umarci magatakardar kotu da ya tantance waɗanda suka tsaya wa waɗanda ake tuhuma kafin a cika sharuɗɗan belinsu. A halin yanzu, kotun ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare su a gidan gyaran hali na Kuje.
An ɗage ci gaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 22 ga Yulin 2026.
A halin yanzu, hukumomi na zargin Timipre Sylva da kasancewa cikin waɗanda ake bincike kan wani yunƙurin juyin mulki da ake zargin an shirya wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Sylva dai bai fito fili ya mayar da martani kan waɗannan zarge-zarge ba.