Ministan Matasa na Najeriya, Ayodele Olawande, ya bayyana cewa har yanzu gwamnatin tarayya ba ta yanke hukunci kan sauya tufafin masu yi wa ƙasa hidima na NYSC daga kakin da ake amfani da shi zuwa zanin Adire ko Kampala ba.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, ministan ya ce rahotannin da suka ce an riga an amince da maye gurbin kakin NYSC da Adire sun fassara kalamansa ba daidai ba bayan wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels.
Ya bayyana cewa a lokacin hirar ya ambaci Adire da Ankara ne kawai a matsayin wasu daga cikin shawarwarin da ake tattaunawa a kansu, ba wai a matsayin tsarin da gwamnati ta amince da shi ba.
"Manufata ita ce in bayar da misalai na wasu daga cikin shawarwarin da aka gabatar yayin tattaunawa. Ban sanar da cewa an amince da wani irin kaya ya maye gurbin kakin NYSC na yanzu ba," in ji ministan.
Olawande ya ƙara da cewa duk wata matsaya da za a cimma za ta biyo bayan cikakkiyar tattaunawa da masu ruwa da tsaki, tare da la'akari da abin da ya fi amfani ga shirin NYSC da kuma ƙasa baki ɗaya.
Ya kuma yi kira ga jama'a da kada muhawarar da ake yi kan kayan NYSC ta karkatar da hankali daga manyan sauye-sauyen da gwamnati ke shiryawa domin inganta shirin, ƙarfafa matasan Najeriya, da kuma bunƙasa ci gaban ƙasar.