Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewa yawancin sojojin Amurka da aka tura ƙasar a farkon wannan shekarar domin taimakawa wajen yaƙi da ta'addanci sun janye daga ƙasar.

Kakakin rundunar sojin Najeriya, Michael Onoja, ya shaida wa BBC cewa janyewar sojojin ba za ta kawo cikas ga ayyukan tsaron Najeriya ba.

"Ba zai shafi yadda muke tafiyar da harkokinmu ba. Za mu ci gaba da musayar bayanan sirri," in ji Onoja.

Kalaman nasa sun yi daidai da na kwamandan rundunar sojin saman Amurka a nahiyar Afirka (AFRICOM), Janar Dagvin Anderson, wanda ya bayyana cewa duk da janyewar dakarun, haɗin gwiwar ƙasashen biyu ta fuskar musayar bayanan sirri da sauran fannoni zai ci gaba.

Najeriya na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro da suka haɗa da hare-haren ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi, ƴan bindiga masu garkuwa da mutane, da rikice-rikicen da suka bazu daga yankin Arewa zuwa Tsakiyar Najeriya da wasu sassan Kudancin ƙasar.

Haɗin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka ya ƙara ƙarfi a cikin watannin baya, musamman bayan gwamnatin Amurka ta nuna damuwa kan halin tsaro a Najeriya. Sai dai gwamnatin Najeriya ta musanta wasu zarge-zargen da ke cewa ana gudanar da "kisan ƙare dangi" kan Kiristoci, tana mai cewa rikice-rikicen tsaron da ake fuskanta suna da sarkakiya kuma suna shafar al'ummomi daban-daban ba tare da bambanci ba.

Tun daga watan Disamban shekarar da ta gabata, dakarun Najeriya da na Amurka sun gudanar da jerin ayyukan haɗin gwiwa da suka haɗa da kai farmaki kan maɓoyar ƴan bindiga da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya, a wani ɓangare na ƙoƙarin inganta tsaro a faɗin ƙasar.