Iran ta fara gudanar da zaman makoki na ƙasa baki ɗaya yayin da ake shirye-shiryen jana'izar tsohon Jagoran Addinin ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei, wanda aka kashe fiye da watanni huɗu da suka gabata a hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai.
Hukumomi sun bayyana cewa za a ajiye gawarsa a babban ɗakin taro na Grand Mosalla da ke birnin Tehran daga ranar Juma'a, inda jama'a za su samu damar yi masa bankwana, kafin a kai gawar zuwa garinsu na Mashhad domin binne shi a ranar Alhamis mai zuwa.
A cewar kamfanin dillancin labarai na AFP, ana sa ran sama da mutane miliyan 20 daga sassa daban-daban na Iran za su halarci jana'izar.
Shirye-shiryen jana'izar na gudana ne a daidai lokacin da Iran da Amurka ke ci gaba da tsagaita wuta bayan cimma yarjejeniyar dakatar da faɗa da suka sanya wa hannu a watan Yuni.
Hukumomi sun ce za a ajiye gawar Khamenei a Grand Mosalla na tsawon kwanaki uku tare da gawarwakin wasu daga cikin 'yan uwansa da aka kashe a hare-haren.
An tsara gudanar da babban taron jana'izar a hukumance a birnin Tehran ranar Asabar.
Rahotanni sun kuma ce gwamnatin Iran ta umarci a rufe ofisoshin gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu a Tehran daga ranar Asabar zuwa Litinin domin sauƙaƙa gudanar da jana'izar, tare da kafa takunkumin zirga-zirga a wasu sassan tsakiyar birnin.