Aƙalla mutum shida sun mutu, yayin da wasu 22 suka jikkata sakamakon fashewar wani bam a wani gidan shan shayi da ke cike da jama'a a tsakiyar birnin Damascus, babban birnin ƙasar Syria.
Kafafen yaɗa labaran gwamnatin Syria sun ruwaito cewa, bam ɗin ya tashi ne a wani gidan shan shayi da ke gundumar Hejaz, mai nisan kusan mita 100 daga ginin Ma'aikatar Shari'a ta ƙasar.
Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta Syria ta bayyana cewa an dasa abin fashewar ne a cikin gidan shayin kafin ya tashi, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da jikkata mutane da dama.
Har zuwa yanzu babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin harin kai tsaye. Sai dai wannan shi ne harin bam mafi muni da aka kai a Damascus tun bayan harin ƙunar baƙin wake da aka kai a wani coci a watan Yunin 2025, wanda ya kashe mutane 25.
Ko da yake wata ƙungiyar masu iƙirarin jihadi mai suna Saraya Ansar al-Sunnah ta yi ikirarin cewa ita ce ta kai harin na baya, hukumomin Syria sun dora alhakin hakan kan ƙungiyar IS.
Wani mazaunin yankin, Mohammed al-Dahabi, mamallakin wani shagon sayar da gilashi da ke kusa da wurin da lamarin ya faru, ya ce fashewar ta tuna masa da hare-haren da aka saba gani a lokacin yaƙin basasar Syria.
Bayan kai ziyara wurin da harin ya faru, gwamnan Damascus, Maher Marwan Idlibi, ya tabbatar da cewa hukumomi sun fara bincike tare da alƙawarin gurfanar da duk waɗanda aka samu da hannu wajen shirya harin a gaban doka.