Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya sha alwashin sallamar duk wani ma'aikacin gwamnati da aka samu ya samu aiki ta hanyar amfani da takardun bogi.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin wani taro a jihar, inda ya ce ba za a lamunci cuwa-cuƙwar takardun neman aiki ba, musamman a ɓangaren ilimi, saboda hakan na da illa ga ci gaban jihar.

"Wanda ya yi cuwa-cuƙwar takarda aka ɗauke shi aiki, ba shi da aiki... siyasa kuma idan ya ga dama ya je ya zaɓi Fir'auna," in ji Gwamna Radda.

Ya ƙara da cewa:

"In ba da ka da takarda aka kore ka aiki sai me? Ko gobe muka kama wanda ba shi da takarda, korar sa za mu yi."

A cikin wani gajeren bidiyo da Katsina Post ta wallafa a shafinta na Facebook, gwamnan ya soki abin da ya kira siyasantar da harkokin ilimi, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta yi sassauci ga duk wanda aka tabbatar ya samu aiki da takardun bogi ba.

Kalaman gwamnan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da gudanar da tantance ma'aikata a jihar, matakin da ya haifar da muhawara da ƙorafe-ƙorafe daga wasu ma'aikata da masu ruwa da tsaki tun bayan hawansa mulki.